‘Yan Sanda Sun Fara Cin Gajiyar Sabon Albashi

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta ce ta fara biyan Jami’an ‘yan sandan kasar sabon tsarin albashi da ta gyara musu.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ranar Alhamis a shafinta na Tuwita.

Tun a cikin watan Nuwambar 2020 ne gwamnatin kasar ta yi alkawarin inganta tsarin albashin jami’an ‘yan sandan kasar.

Dama dai ‘yan kasar da dama, da ma su kansu ‘yan sandan sun sha korafe-korafen cewa albashin da gwamnatin kasar ke biyansu ya yi kadan.

Labarai Makamanta