‘Yan Sanda Su Karbi Ragamar Yaƙi Da Boko Haram -Gwamnoni

Kungiyar gwamnonin Arewa Maso Gabas sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tura ‘yan sanda don yakar Boko Haram a yankin, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a wata takarda da ta fitar bayan taronta karo na biyu da tayi don tattaunawa a kan kalubalen da yankin ke fuskanta.

Takardar ta samu saka hannun shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.

Ta jinjinawa kokarin gwamnatin tarayya wurin yaki da ta’addancin, amma tayi kira ga dakarun soji da su tsananta tsaro wurin tabbatar da cewa manoma a yankin za su iya komawa gonakinsu.

Kungiyar ta bukaci cewa , a rufe gibin rashin ma’aikata isassu ta hanyar tura jami’an ‘yan sanda don tsaro sannan a samar musu da kayayyakin aiki isassu,” takardar tace.

Ta yi kira ga ma’aikatar ruwa ta tarayya da ta mayar da hankali wurin cike tafkin Chadi tare da karfafa sauran rafukan da ke yankin.

Takardar ta ce, gwamnonin shida sun dauka alwashin aiki tare don tabbatar da hadin kai, ci gaba da habakar yankin ballantana a fannin hako man fetur, noma da kuma masana’antu.

Takardar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kwace ayyukan tituna da ma’aikatar ayyuka ta bada na tsawon shekaru ba tare da an yi ba sannan ta bai wa ‘yan kwangilar da suka shirya yi.

Labarai Makamanta