Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

‘Yan Najeriya Za Su Sauke Farali A Bana – Hukumar Alhazzai

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar jin dadin alhazai ta ƙasa NAHCON ta bayyana cewa da yardar Ubangiji bana maniyyata a Najeriya zasu samu zuwa kasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajjin Bana.

Wannan ya biyo bayan soke dokokin kariya daga cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Saudiyya tayi a farkon makon nan.

Kwamishanan hukumar mai wakiltar al’ummar yankin kudu maso kudu, Musa Sadiq Oniyesaneyene ya bayyana hakan a hirarsa da Legit Hausa ya bayyana cewa ko makwannin baya ya shiga Saudiyya kuma da yardar Allah bana za’a tafi.

“Dubi ga yadda abubuwa ke gudana yanzu, Insha Allahu ya kamata ayi kuma za’a yi. ‘”Saboda sassauta dokokin kariya daga cutar Korona a Saudiya da kuma maganar cewa an cire dokar kayyade maniyyata masu shiga Harami, tabbas za’a yi Hajji.”

“Ko watanni biyu da suka gabata na tafi Saudiyya wasu ayyuka, mun fuskanci matsaloli, ni kaina na fuskanci wadannan matsaloli amma sai da aka tilasta ni zama a Madina cikin dakin Otal, hakazalika a Makkah.” “Amma muna kyautata zaton cewa yanzu an cire wadannan dokoki.” Insha Allahu bana yan Najeriya zasu yi aiki Hajji.

Hukumomi a Masallatai biyu mafi daraja a duniya sun yi watsi da dokar wajabta baiwa juna tazara yayin Sallah a Masallacin Haram dake Makkah da Masjid Al Nabawi dake Madina.

Exit mobile version