‘Yan Najeriya Sun Matsa Mini In Fito Takarar Shugabancin Kasa – Bello

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya ce yana cigaba da samun kiraye kiraye da matsin lamba daga ‘yan Najeriya na cewar ya fito domin neman Shugabancin ƙasa a 2023 “dukkan ‘yan Najeriya” ne suke bukatata da in nemi kujerar shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa.

A yayin jawabi a ranar Juma’a yayin da ake yin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels, Bello ya ce zai bada amsa ga wannan bukatar nan babu dadewa.

Gwamnan yace ‘yan Najeriya suna bukatar dan takara da zai hada kan kasar nan, kuma ya yadda yana da dukkan nagartar da ake bukata domin zama shugaban kasa.

“Matasa da mata tare da dukkan ‘yan Najeriya suke rokona da in tsaya takarar shugaban kasa a 2023. Kuma na yadda cewa lokaci yayi da zan duba ko zan iya. Waye zai iya hada kan kasar nan? Ina tunanin suna ganin wani abu a tare da ni ne shiyasa suke son in zo in hada kan kasar nan kuma in gyarata,”.

“Nan babu dadewa zan amsa musu. Ina kira ga kowa da kowa dake yi min wannan kiran na takarar shugabancin kasa da su yi hakuri. “Har yanzu akwai aikin da nake kuma da izinin Ubangiji, ba zan baku kunya ba idan lokacin yanke hukuncin zan fito takara ko ba zan fito ba yayi.”

Labarai Makamanta