‘Yan Najeriya Milyan 54 Ne Ke Fama Da Baƙin Talauci – Hukumar Ƙididdiga

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), ta fitar da lissafin cewa akwai kashi 27.1 na yawan ‘yan Najeriya da ba su da aikin yin da za su rika samun kudin abincin yau ko na gobe.

Wannan kididdiga na nufin idan yawan jama’a a Najeriya sun kai milyan 200, to milyan 54,200 ba su da aikin yi, kuma basu da abincin yau da na gobe.

NBS ta ce wannan Kididdiga ta yawan adadin wadanda aka tabbtar ne a watannin Aprilu, Mayu da Yuni na cikin 2020.

Rabon da NBS ta yi wannan kididdiga tun wadda ta yi cikin watannin Yuli, Agusta da Satumba na 2018, inda a lokacin aka samu kashi 23.1 na ‘yan Najeriya duk ba su da aikin yi.

Kafin wannan kuwa a lissafin watannin Oktoba, Nuwamba da Disamba, 2018, kashi 18.8 ba su da aikin yi.

Ya zuwa watanni ukun tsakiyar 2018 ne adadin ya karu zuwa kashi 23.1, sai kuma yanzu cikin 2020 da adadin ya karu zuwa kashi har 27.1.

Annobar cutar Coronavirus ta zuzuta matsalar tabarbarewar tattalin arziki, inda manyan masana’antu suka rika sallamar ma’aikatan su, wasu kuma su ana zaftare musu albashi.

NBS ta ce yawan majiya karfin iya aikin neman kudi a Najeriya sun karu daga mutum milyan 111.1 cikin 2017 zuwa milyan 115.5 cikin tsakiyar 2018.

Sai dai kuma NBS ba ta fadi adadin yawan cima-zaunen da ke Najeriya ba, ballantana a san yawan su.

Hukumar NBS, wato National Bureau of Statistics, hukuma ce ta gwamnatin tarayya wadda aikin ta shi ne kididdigar rashin aikin yi, matsin tattalin arziki, hawa da tashi ko saukar farashin kayan abinci da na masarufi da kuma duk wani nau’in tsadar rayuwa.

Sannan aikin NBS ne kididdigar yawan ‘yan Najeriya maza da yawan mata, yawan yawan magidanta, yawan cima-zaune, wato ‘yan jarirai zuwa ‘yan shekara 15 da kuma dattawa ‘yan shekaru 66 zuwa sama.

Labarai Makamanta