‘Yan Najeriya Miliyan 133 Na Fama Da Matsanancin Talauci – Gwamnatin Tarayya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kashi 63 cikin 100 na ƴan ƙasar, wato mutum miliyan 133 na cikin talauci.

Alƙaluman binciken ma’aunin talauci a Najeriya ne suka tabbatar da hakan a ranar Alhamis a Abuja.

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa da hukumar tsara bayar da tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi da shirin samar da ci gaba na majalisar ɗinkin duniya da asusun ilimin ƙanana yara na Unicef da shirin yaƙi da talauci da cigaban al’umma na Oxford ne suka gudanar da aikin ƙididdigar.

Binciken ya nuna cewa an karɓi bayanan magidanta dubu 56 a sassan jihohin ƙasar 36 da birnin tarayya Abuja, da aka gudanar tsakanin watan Nuwamban 2021 zuwa Fabarairun 2022.

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa kashi 65 cikin 100 na matalauta a ƙasar na rayuwa ne a arewacin Najeriya, yayin da kashi 35 cikin 100, kusan mutum miliyan 47 ke nan na zama ne a kudanci.

Sokoto ce jihar da ta fi fama da talauci a ƙasar, inda kashi 91 cikin 100 na al’ummarta ke rayuwa hannu-baka hannu-ƙwarya, Ondo ce kuma mafi ƙarancin talauci a Najeriya da kashi 27 cikin 100.

A lokacin da ya yi tsokaci kan alƙaluman, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wannan bayani zai bijiro da hanyoyin da za a bi wajen yaƙi da talauci.

A wani labarin na daba hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewa ‘yan Najeriya miliyan 19.4 ne za su yi fama da yunwa da barazanar rashin abinci a watannin Yuni zuwa Agustan bana.

Hukumar ta yi wannan bincike tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Gona ta Tarayya da wasu Cibiyoyi masu ruwa da tsaki a harkar noma.

Rahoton ya yi nazarin matsalar ƙarancin abincin da za a fuskanta da kuma rashin abinci mai gina jiki a yankunan Sahel da Afrika ta Yamma.

Labarai Makamanta