‘Yan Najeriya Basu Buƙatar Izini Kafin Zama Inda Suke So – Bala

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, yace mutane Yan asalin Najeriya basu bukatar neman izinin gwamnatin Jiha ko ta Tarayya kafin su zauna a kowani wuri a dukkan fadin kasan.

Gwamnan yayi wan nan furucin ne a kafar watsa labarai na talabijin din (Channels) a jiya Jumma’a, sakamakon cece kuce da akayi tayi akan kalaman sa da yayi a bikin mako na masu dauku rahotanni daga Jihar Bauchi.

Kalaman dai sun harzuka wadansu shuwagabanin da kuma kungiyoyi a ciki da wajen Najeriya, suna cewa shi Gwamna Bala yace makiyaya zasu iya daukar makamin AK 47 don kariya ga rayuwarsu. Yace kalamai ne na furuci, ba ina goyon bayan aikata laifi bane

“Ba wai su dauki hukunci a hannun su ba, duk wanda ya aikata laifi to akamashi a hukunta shi, shine adalci amma ace su bar jeji, babu wanda yake da ikon hana dan Najeriya zama a inda yake so”

A lokacin da yake maida martani a kafar talabiji din, Gwamna Bala yace shuwagabbani ya kamata su fitar da hanyar samar da zaman lafiya ga kowani diron Najeriya.

Kana Gwamna Bala ya kara da cewa abunda suka yi na cewa makiyaya su bar yankin jejin kudancin kasan nan, ya saba ma tsarin kundin mulkin Najeriya a cikin sashe na 41, saboda in haka, nace makiyaya Fulani masu kiwon shanu an cinye masu hanya da suke bi, da kuma ke shanunsu ke cin abinci.

Basu da wata harka ta rayuwa sai kiwo, ya ake so suyi, ga matsatsin da suke shiga na yan’fashi daji, da sace masu shanu, basu da kariya, ga Kuma tsangwama daga sauran dai-dai kun jama’a, saboda haka yin hakan bashi da wani alfanu

Abun da na fada a gaban Yan’jarida a ranar kammala bikinsu na mako a Jihar, dama akan aikin Jarida na amfani da aiki wajen kawo zaman lafiya a Najeriya” Kuma nayi kokari ne in fito da matsalar a fili kowa ya sani”. Gwamnan ya fada.

Kana ya karkare da cewa gwamnoni su tashi tsaye don gano mafita ba su zauna suna kokarin korar wasu ba, yace wanda yayi laifi ya fuskanci hukunci don adalci ma kowa kar a kore su don su ba yan yankin bane, shine zai kawo zaman lafiya a Najeriya kan wan nan matsala ta makiyaya.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta