‘Yan Najeriya 636 Aka Kashe Cikin Wata Guda – Bincike

Wani rahoto game da matsalar tsaro a Najeriya ya ce an kashe mutum 636 a watan Oktoba kaɗai a sassan Najeriya.

Kamfanin Beacon Consulting duk wata yakan fitar da rahoto kan binciken da ya yi game da matsalar tsaro a Najeriya tare da bayar da shawarwari ga mahukunta.

Rahoton kamfanin ya ce alƙalummansa sun shafi jihohi 33 na Najeriya a ƙananan hukumomi 105.

Rahoton ya nuna yadda kamfanin gudanar da nazari da bincike da tattara alkalumansu a watan Oktoba. Da kuma girman barazanar kai hare-hare a arewacin Najeriya duk da matakan da gwamnatin tarayya ke dauka da jihohi.

Alƙalumman sun nuna an samu raguwar yawan adadin waɗanda aka kashe a Najeriya a watan Oktoba idan aka kwatanta da rahoton watan Satumba inda alƙalumman suka ce an kashe mutum 663.

Sai dai rahoton ya ce wata na huɗu kenan a jere da aka samu sama da mutum 600 da aka kashe a Najeriya tun a Yuni, watan da aka fi kashe mutane a Najeriya a 2021 inda aka kashe mutum 1031.

A cewar rahoton kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito alƙaluman sun haɗa da yawan mutanen da aka kashe sakamakon rikicin Boko Haram, da kuma na ƴan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya da ma waɗanda jami’an tsaro suka kashe a bakin aiki, da kuma su kansu jami’an tsaro da suka rasa rayukansu a fagen daga.

Da kuma ƙaruwar laifuka a yankin kudu maso yammacin Najeriya da ya haɗa da fasa gidan yari da aka yi a jihar Oyo da tasirin yunƙurin Najeriya na hukunta shugaban ƴan a waren Biafra Nnamdi Kanu wanda ke ƙara ingiza mambobin IPOB da ƙaruwar rikici a kudu maso kudu da kudu maso gabas.

Rahoton ya bayyana cewa yanayin ya sauya daga arewaci zuwa kudanci, inda kudu maso yammaci da kudu maso gabas aka samu ƙaruwar kashi 22 idan aka kwatanta da kashi 19 a arewa maso yammaci da arewa ta tsakiya. Kudu maso kudu da arewa maso gabas an samu ƙaruwar kashi tara.

Sai dai duk da sauyin, adadin waɗanda aka kashe bai sauya ba, inda a arewa maso yammaci aka kashe mutum 258, a arewa maso gabas mutum 158.

A yankin arewa ta tsakiya mutum 109 aka kashe, a kudu maso gabas mutum 65, yayin da a kudu maso yammaci aka kashe mutum 30, mutum 16 a kudu maso kudu.

Amma rahoton ya ce an samu raguwar matsalolin tsaro a arewa maso yammaci da kashi 47 tsakanin Satumba zuwa Oktoba, haka ma a arewa ta tsakiya da kashi 39.

Amma a cewar rahoton an samu ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga a kudu maso gabas da kashi 71 da kashi 19 a kudu maso yammaci.

Rahoton ya kuma ce an samu raguwar hare-haren ƴan bindiga masu fashin daji a jihohin Kaduna da Katsina da Sokoto da Zamfara saboda matakan da hukumomi suka ɗauka na tsaro da suka haɗa da katse hanyoyin sadarwa da hana cin kasuwannin maso da kuma ayyukan hakar ma’adinai.

Sai dai kuma a cewar rahoton an fi samun ƙaruwar hare-haren a jihar Sokoto a watan Satumba duk da matakan da aka ɗauka.

Rahoton na ƙwararru ya ce duk da matakan da jihohi huɗu suka ɗauka na arewa maso yammaci kan matsalar hare-haren ƴan fashi, ya sassauta hare-haren amma akwai buƙatar a ɗauki mataki na bai-ɗaya a yankin kamar sa ido a kan iyakoki da neman haɗin kan hukumomin Nijar da ke makwabtaka a jihohin na Najeriya.

Binciken ya yi barazanar cewa hare-haren da satar mutane za su ƙaru saboda halin matsi na tattalin arziki da ake ciki a Najeriya da kuma tsadar farashin kayyaki a ƙasar.

Rahoton ya yi kira ga hukumomin ƙasar su fara yin ƙoƙarin magance rashin yardar da ta yi katutu a tsakanin ‘yan ƙasar da nufin daƙile yawan kashe-kashen mutane da ake fama da shi.

An kuma bukaci hukumomi su ɓullo da matakan inganta tsarin zamantakewar da ya taɓarɓare musamman a arewacin Nijeriya da kuma tabbatar da hukunci ga masu aikata laifuka a kasar.

Labarai Makamanta