‘Yan Matan Chibok Sun Cika Shekaru 7 A Hannun Boko Haram

Rahotanni daga Maiduguri Fadar gwamnatin Jihar Borno na bayyana cewar a daidai lokacin da ‘yan matan Chibok suka cika shekaru 7 a hannun Boko Haram, Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce da sannu za’a ceto dalibai matan da yan ta’addan Boko Haram suka sace a makarantar sakandaren Chibok a 2014.

Zulum ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar bayan shekaru bakwai da ‘yan Boko Haram sukayi awon gaba da daliban yayinda suke shirin rubuta jarabawar kammala Sakandare.

Duk da cewa an ceto wasu daga cikin yaran, har yanzu akwai sauran daliban na hannun yan ta’addan. A cewar Zulum, a matsayinsa na uba, ba zai iya jure ciwon rasa diya mace tsawon shekaru bakwai hannun yan ta’adda ba.

Ya yi kira ga ayi addu’a ga ‘yan matan Chibok da sauran mutanen dake tsare hannun yan ta’adda su samu yanci.

A cewar gwamnan, “A matsayina na mahaifi, ban tunanin zan iya jure zafin kasancewar diyata hannun yan ta’adda na tsawon shekaru bakwai.” “Gaskiya, gwamma mutum ya rasa diyarsa da ace tana hannun yan Boko Haram.”

“A matsayina na uban kowa a Borno, ban fidda ran za’a ceto sauran yan matan Chibok da sauran wadanda ke rike hannun Boko Haram ba.”

A bangare guda, iyayen ragowar ɗalibai mata 112 da aka sace a makarantar sakandiren mata dake Chibok jihar Borno, sun bayyana cewa suna son ganin ya’yan su kafin su mutu.

Tunda mayaƙan Boko Haram dake biyayya ga Abubakar Shekau suka sace ƴaƴan nasu, wasu daga cikin iyayen sun rasu saboda tashin hankali wasu kuma sun rasu saboda lokaci yayi.

Yau shekara bakwai kenan dai-dai tun sanda mayaƙan Boko Haram ɗin suka kai farmaki GGSS Chibok ranar 14 ga watan Afrilu, 2014, zamanin mulkin tsohon Shugaban kasa Jonathan.

Labarai Makamanta