‘Yan Boko Haram Ne Suka Kai Hari Kurkukun Kuje – Ministan Tsaro

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar kimanin Fursunoni 600 ne suka tsere a yayin harin da aka kai kan gidan yarin Kuje ranar Talata da daddare, kamar yadda Ministan Tsaro Bashir Magashi ya tabbatar wa BBC da safiyar yau Laraba.

Daga cikin fursunonin da suka tsere kimanin 300 sun mika kansu ga hukumomi don radin kansu a yayin da jam’an tsaro suka kamo wasu daga cikinsu.

Mimistan dai ya dora alhakin harin kan kungiyar Boko Haram, saboda a cewarsa akwai kimanin mayakan Boko Haram akalla 64 a gidan yarin.

Magashi ya kuma tabbatar da mutuwar jami’in Civil Defence daya.

Harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar jam’in tsaro na Civil Defence daya.

A halin yanzu dai gidan yarin na karkashin ikon hukumomin kasar. Akwai dai a kalla fursunoni 994 a gidan yarin.

Harin na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da ‘yan bindiga a Katsina suka yi wa kwambar motocin Shugaba Buhari kwanton-bauna a kan hanyarsu ta zuwa garin Daura.

Labarai Makamanta

Leave a Reply