‘Yan Bindigar Dana Ziyarta Basu Da Alaka Da Sace Daliban Kagara – Gumi

Mashahurin Malamin addinin Musuluncin nan mazaunin garin Kaduna Sheikh Dr.Ahmad Gumi, ya ce ‘yan Bindigar da ya hadu da su a jihar Neja sun musanta sa hannu a sace dalibai 27 na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati (GSC), da ke Kagara.

Shehin malamin ya kuma ce ba ya cikin tattaunawar sakin daliban, kawai ya hadu da ‘yan Bindigar ne domin wa’azi da da gargadi a garesu yadda zasu nisanci aikata laifi.

A ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari GSC Kagara da ke karamar hukumar Rafi a Neja, inda suka yi awon gaba da mutane 41 galibinsu dalibai da ma’aikatan makarantar.

Kwana guda bayan harin, Dr. Gumi, wanda aka san shi da samun damar tattaunawa da ‘yan fashin, ya hadu da wasu daga cikinsu a cikin wani sanannen daji a Neja, kum ya yi kiran ayi musu afuwa a gidan gwamnati dake Minna Babban Birnin jihar.

A hirar da ya yi da kamfanin jaridar THISDAY, malamin ya ce haduwar da ya yi da shugabannin ‘yan Bindigar na zaman lafiya ne kawai kuma ba shi da wata alaka da satar mutanen.

“Ni ba na cikin tattaunawar. Mun dai sadu da wasu daga cikin wadannan tsagerun (a jihar Neja), ina kokarin shawo kan su da daina aikata laifin,” “Mun tambaye su game da abin da ya faru sai suka ce sun san kungiyar da ta sace motar bas din sai suka ce za su shiga tsakani don ganin an sake su.

“Amma ga yaran (makarantar), sun ce ba su san wanda ya yi ba saboda lokaci ya yi kusa da za su sani.

Waɗannan ƙungiyoyin da muka sadu da su na iya samun matsala tare da rukunin aikata ɓarna.”amma ya kara da cewa “babban kwamandan kungiyar da muka hadu da shi ya yi alkawarin cewa zai binciko wadanda suka sace yaran sannan a sake su.”

A wani labarin, Gwamnatin Jihar Neja ta ce ta yi nasarar tabbatar da sakin dukkan fasinjojin da aka sace na Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Neja. Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya tabbatar da hakan ta shafin Twitter a ranar Lahadi.

Labarai Makamanta