‘Yan Bindigar Arewa Sun Samu Horo Ne Wajen Tsagerun Neja Delta – Gumi

Mashahurin Malamin addinin musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi ya yi ƙarin haske akan yadda ayyukan ‘yan Bindiga ke gudana, inda ya tabbatar da cewa da akwai dangantaka ta ƙut da ƙut tsakanin ‘yan bindigar da tsagerun Neja Delta, wanda ya kamata gwamnati ta fahimta kuma ta ɗauki matakin sulhu da yafiya domin samun nasara.

Dr. Gumi ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na AIT a ranar Talata 16 ga watan Fabarairu, inda ya bayyana cewa a wurin tsagerun Neja Delta ‘yan bindigar suka samu horo na kisa da yin garkuwa da mutane don haka a musu afuwa kamar yadda aka yi wa Tsagerun Neja Delta.

A cewar malamin, ɓata garin da ke cikin makiyaya tsiraru ne kuma sauran sun dauki makamai ne domin kare kansu bayan an sace musu shanunsu wanda shine ke matsayin ‘man fetur’ din su.

“Ba mu sauya sabon tsari bane kan yadda muke kokarin warware matsalar shiyasa har yanzu muke a nan. Kuma da muke ce afuwa, ba mu nufin duk wanda aka samu da laifin kisa ya tafi haka nan.

“A wurin ‘yan kungiyar MEND suka koyi garkuwa. Ban ga wani banbanci ba. Sune aka fara sace wa dabobinsu. Shanunsu ne man fetur dinsu. Ina iya cewa kashi 10 cikin 100 na makiyaya ne bata gari ba kashi 90 ba, daga karshe sun dauki makamai ne don kada a karar da su.

“Su da kansu za su iya maganin sauran bata garin da ke cikinsu saboda ba su son wani ya janyo musu fitina.” Inji shi.

Labarai Makamanta