‘Yan Bindiga Suna Ta’addanci Amma Ba ‘Yan Ta’adda Bane – Gumi

Mashahurin Malamin addinin musuluncin nan mazaunin Garin Kaduna Sheikh Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi, ya ce ‘yan bindiga suna aikata ta’addanci amma a zahiri su ba ‘yan ta’adda ba ne.

Gumi ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust. Ya ce kiraye-kirayen da ake yi na gwamnati ta ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda ba komai bane face rashin adalci da son zuciya wanda zai haifar da nadama daga baya.

Malamin ya yi wannan furuci ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

“Wannan abin takaici ne ta hanyar rashin adalci da son zuciya. IPOB kungiya ce, ba tana nufin Igbo ba. Boko Haram kungiya ce kuma ba tana nufin Kanuri ba. “Don haka za ku iya ayyana ‘yan Boko Haram a matsayin ‘yan ta’adda, kuna iya ayyana ‘yan IPOB a matsayin ‘yan ta’adda.

A wannan yanayin me za ku ayyana ‘yan bindiga? “’Yan bindiga kwatance ne mara tushe. Me kuke bayyanawa? Kuna so ku ce makiyaya ’yan ta’adda ne?

Wannan daya kenan. Na biyu kuma, yanzu an ayyana IPOB a matsayin ‘yan ta’adda, wane canji aka samu? Amurka, Tarayyar Turai, a ko’ina ba su amince da wannan furucin ba.

“Ba su sanya musu takunkumi ba, ba su hana su tafiye-tafiye ba, ba da gudummawar kudi ba, watakila saboda ba mu ba ne, su ne. “Kuma a wannan yanayin, idan kuka ce Fulani makiyaya ‘yan ta’adda ne domin wannan ita ce maganar da kuka fada, ba za ku iya cewa ‘yan bindiga ‘yan ta’adda ba ne, ‘yan bindiga suna aikata ta’addanci amma su ba ‘yan ta’adda ba ne.”

Kashe-kashen da ake yi wa Fulani ba bisa ka’ida ba shi ne babban abin da ke kara rura wutar rikicin ‘yan bindiga a kasar nan. Ya kara da cewa: “Za a iya kama Bafulatani da bai ji ba bai gani ba bisa zarginsa kuma ya rasa shanunsa, kamar yadda ‘yan bindiga za su yi garkuwa da wanda bai ji bai gani ba, ya rasa dukiyarsa.

“Don haka duk mutanen da ke rike da bindigogi a yanzu suna da alhakin cin zarafi da cutar da mutane, ko dai a bangaren gwamnati ko kuma a bangaren ‘yan Bindigan”

Labarai Makamanta