‘Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Sace Gawar Deligate Da Ya Mutu A Abuja

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ‘Yan bindiga sun sake tare babban titin Abuja zuwa Kaduna ranar Talata domin garkuwa da matafiya da aiwatar da kisan kai.

Rahotanni sun bayyana cewar daga cikin wadanda harin ya kusa rutsawa da su akwai wadanda suke ɗauke da gawar Deleget din Jihar Jigawa da ya rasu a taron APC, sai da suka canza hanya suka koma ta Nasarawa zuwa Filato zuwa Bauchi sannan zuwa Jigawa

An yi yunkurin awon gaba da gawar Isah Baba-Buji, deleget din jihar Jigawan da ya mutu wajen zaben fidda gwanin yan takaran kujeran shugaban kasa na jam’iyyar APC a Abuja.

An ruwaito cewa an yi kokari sace gawar ne yayin da take hanyarta zuwa Jigawa don jana’iza. Marigayin ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Arewa maso yamma.

Labarai Makamanta