‘Yan Bindiga Sun Yi Ta’asa A Jihar Kogi

Rahotanni daga Lokoja babban birnin Jihar Kogi na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun hallaka kwamishinan hukumar fansho na jihar Kogi, Solomon Akeweje.

An ruwaito cewa an kashe shi ne da yammacin ranar Asabar yayin da yake dawowa daga Ilorin zuwa Kabba.

An ce ‘yan bindigan sun harbi motarsa a Eruku, tazarar kilomita kadan daga Egbe a jihar.lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar shi nan take.

Har yanzu ba a san inda Shugaban Karamar Hukumar Yagba ta Yamma, Pius Kolawole yake ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoton, kasancewar suna tare da Akeweje lokacin da lamarin ya faru.

An gano cewa Kwamishinan Hukumar ta Fansho ya mutu ne bayan harsasai sun same shi. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ayuba Ede, ya ce “lamarin ya faru ne a Eruku general area na jihar Kwara “. Ya ce ana kuma ci gaba da bincike kan lamarin.

Labarai Makamanta