‘Yan Bindiga Sun Yi Mummunan Ta’asa A Sabon Harin Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu gungun ‘yan Bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai ma wasu garuruwa biyu hari a yankin ƙaramar Hukumar Zangon Kataf dake jihar, inda suka karkashe mutane tare da kone gidaje masu yawa.

Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, wadda aka rarraba ta ga manema labarai a Jihar.

“Sojoji da yan sanda sun sanar da gwamatin jihar Kaduna kan hare-haren da aka kai a Yagbak da Ungwan Ruhugi a karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna. “A cewar rahotannin, an kashe wasu mutane sannan an yi wa wasu rauni, yayin da aka kona wasu gidaje da dukkan garuruwan biyu.”

Gwamnatin na jihar Kaduna ta yi kira mutanen jihar su kwantar da hankulansu a yayin da ake jiran cikaken rahoto daga rundunar sojoji, yan sanda da DSS, za a cigaba da sanarwa mutanen gari abin da ke faruwa da zarar an tabbatar da cikakken rahoto.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi Allah wadai da harin sannan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, sannan ya umurci hukumar jihar na bada taimakon gaggawa, SEMA, ta yi nazarin asarar da aka yi ta tallafawa mutanen.

Labarai Makamanta