Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar kungiyar mutanen kudancin Jihar wato SOKAPU ta yi zargin cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da sama da mutum 40, harda ‘yan coci a kwatas din Bayan Kasuwa da ke Kasuwan Magani, karamar hukumar Kajuru dake jihar ta Kaduna.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dr. Awemi Maisamari,ya gabatarwa manema labarai a Kaduna a ranar Litinin, ya ce yan bindigar sun tuntubi yan uwan wadanda aka sace inda suke nemi a biya naira miliyan 200 kafin su sake su.
A cewar kungiyar, lamarin ya afku ne a ranar 12 da 13 ga watan Satumba, a yankin Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru, yan kilomita daga cikin birnin. Maisamari ya bayyana cewa har yanzu garuruwan da ke kudancin Kaduna na jihar basu da sukuni domin yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare kan mazauna.
“Har yanzu babu sauran sukuni ga garuruwan da ke kudancin Kaduna. Yan ta’adda, yan bindiga da makiyaya masu makamai suna ci gaba da kai munanan hare-hare a garuruwan da ke kudancin jihar.
“Harin baya-bayan nan sune na sace mutane da dama da aka yi a ranar 12 da 13 ga watan Satumban 2022 a Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru na Kudancin Kaduna. “Kasuwan Magani na kimanin kilomita 20 daga garin Kaduna a kan babban titin Kaduna-Kafanchan da kuma a nan ne babbar kasuwar mako na jihar Kaduna take.
“A ranar farko 12 ga watan Satumba, mutum shida aka sace a farmakin dare da yan bindigar suka kai yankin Ungwan Fada da ke garin. “Ba tare da an dauki mataki don gudun sake faruwar hakan ba, washegari, 13 ga watan Satumba, yan bindigar sun farmaki cocin Cherubim da Seraphim Church, a yayin addu’an dare a kwatas din Bayan Kasuwa da ke garin Kasuwan Magani da tsakar dare.
“Sun dauke fiye da mutum 60 daga cocin da gidajen da ke makwabtaka. Sai dai kuma basu yi nsarar wucewa da dukkansu ba saboda wasun su yara ne sosai, wasu sun tsufa wasu kuma suna da lalura.” Ya kuma kara da cewa zuwa yanzu an tabbatar da sace mutum 45.
“Jiya, 18 ga watan Satumba, masu garkuwa da mutanen sun tuntubi wasu mutane a garin ta wayar tarho kuma sun yi ikirarin cewa mutum 40 kawai ke tsare a hannunsu.
You must log in to post a comment.