‘Yan Bindiga Sun Yi Kisan Kiyashi A Zamfara

Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Zamfara na bayyana cewa wasu gungun ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kashe gwamman mutane a jihar.

Ƴan bindigar waɗanda suka je garuruwan Anka da Bukkuyum a kan babura masu ɗumbin yawa, sun afka ƙauyukan da ke ƙarƙashin waɗannan garuruwan inda suka rinƙa harbi kan mai uwa da wabi tare da cinna wa gidaje wuta.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mutanen da ƴan bindigan suka kashe sun haura mutum 100. Wani wanda ya shaida lamarin ya shaida wa BBC cewa ya ga gawa ta mutum takwas a wani ƙauye.

An bayyana cewa ƴan bindigan sun soma kai harin tun daga ranar Talata da dare har zuwa Laraba inda ƴan bindigan suka ci gaba da kutsawa daga wanan ƙauye zuwa wancan.

Labarai Makamanta