Rahotannin dake shigo mana daga ƙaramar Hukumar Ƙanƙara ta Jihar Katsina na bayyana cewar wasu ‘yan Bindiga bisa Babura ɗauke da muggan makamai sun kutsa wata majami’a inda suka yi awon gaba da tarin wasu mutane da ke gudanar da Ibada a a ciki.
Shugaban cocin Katolika na ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina, Ravaran Yusufa Haruna ya tabbatar da sace masu ibada tara a ƙauyen Gidan Haruna.
A cewarsa, maharan sun jikkata mutum ɗaya a harin da suka kai a ƙarshen mako.
Ya ce “ƴan ta’adda sun zo suka same su suka tafi da mutum bakwai da yara guda biyu kuma sun bugi wani da sanda sun karya shi a hannu.”
Kuma duk da iƙirarin hukumomi cewa suna murƙushe ƴan fashin da sauran ƴan bindiga, har yanzu mazauna ƙauyuka da wasu garuruwan ƙasar na ci gaba da ɗanɗana kuɗa a hannun irin waɗannan ɓatagari.
You must log in to post a comment.