‘Yan Bindiga Sun Tada Garuruwa A Kaduna

Rahotannin dake shigo mana yanzu daga Jihar Kaduna na bayyana cewar akalla mutum huɗu ne suka rasu sannan ƴan bindiga suka yi awon gaba da wasu da dama a garuruwa daban-daban na yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna cikin kwana biyu da suka gabata.

Ana kyautata zaton ƴan bindigar da aka koro daga jihar Zamfara ne ke cin karensu babu babbaka a yankin, inda yanzu haka jama’ar garuruwan ke ta barin gidajensu.

Malam Zubairu Abdul’rauf mazaunin yankin ne kuma ya shaida wa BBC Hausa cewa rayuwa a yankin Birnin Gwari na sake yin tsanani ga al’ummar wajen.

A cewarsa, zuwa wayewar garin Litinin ƴan bindigar sun kora al’ummar ƙauyuka kamar Sabon Gida da Rema da Aworupo da wasu ɓangare na Dagara – wato kusa da Dajin Kuyambana – inda suka bar muhallansu.

“An kashe mutum huɗu, an kwashe mata uku da maza da dama. Su matan an ɗauke su ne a garin Sabon Gida suna tsaka da yin biki.

“A ƴan kwanakin nan ana zaton ƴan bindigan da ake kora daga Zamfara ne suke sake shiga yankunan ƙaramar hukumar Birnin Gwari suna wannan ta’asa,” in ji Zubairu.

Mazaunin Birnin Gwarin ya ƙara da cewa: “Wannan abu ya ta’azzara cikin kwana biyar da suka gabata. Bayan da ƴan bindigar suka kai hari suka kwashi na kwasa suka kashe na kashewa, sai suka ƙona gidajen ƙauyukan da rumbunan abinci.

“To wannan dalili ne ya sa mutanen garuruwan suka watse suka zama ƴan gudun hijira a wasu wuraren. Wasu sun koma kusa da Madatsar Ruwa ta Bagoma, wasu kuma sun koma cikin garin Birnin Gwari,” a cewarsa.

Mazauna yankin sun kuma ce hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna ta zama tamkar tarkon mutuwa don bin ta kawai ake yi saboda babu tabbas a kowane lokaci.

Ko a ranar Talata ‘yan bindiga sun tare hanyar sun kwashi mutane da dama da ba a san adadinsu ba, a cewar rahotanni.

“Duk da cewa suna tafiya ne ƙarƙashin rakiyar jami’ar tsaro. Bari suke sai motocin gaba-gaban sun fara wucewa sai su fito su datsi na tsakiya da na ƙarshe su buɗe wuta, duk da cewa akwai jami’an tsaro a ayarin, sai su kwashi na kwasa,” in ji Zubairu Abdulra’uf.

Wani abu da mutane za su tambayi kansu shi ne; ko ta yaya mutanen Birnin Gwari ke samun ababen jin daɗin rayuwa, tun da sai daga Kaduna suke iya samu, ga kuma yanayin hanya?

Mazauna yankin sun ce rayuwa ta yi tsada sosai saboda yana yi wa ‘yan kasuwa wahalar zuwa Kaduna a-kai-a-kai, sannan su kansu manoma ba su da hurumin yin noma yadda ya kamata balle abinci ya wadata.

“Sai ‘yan tsiraru da suka biya ‘yan bindiga wasu kuɗaɗe sannan su ƙyale su suka girbi amfanin gonar tasu. Ana dai cikin halin ha’ula’i”, a cewarsa.

Labarai Makamanta