‘Yan Bindiga Sun Taba Garkuwa Da ‘Ya’yana Sai Da Na Biya Kudin Fansa – Gumi

Shahararren malamin addinin Islaman nan mazaunin Garin Kaduna Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa shi ma ya sha fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke addabar arewa.

Ya ce an yi garkuwa da yayansa kuma sai da ya biya kudin fansa domin a sake shi. Malamin na Kaduna ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba.

Gumi ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan zargin da ake masa na daukar nauyin ‘yan bindiga da kuma tallafa musu.

Malamin ya sha neman gwamnatin tarayya da ta yi wa ‘yan bindiga afuwa, ya ce ba daidai bane a ce yana goyon baya ko daukar nauyin miyagu.

Labarai Makamanta