‘Yan Bindiga Sun Sake Tafka Mummunan Ta’asa A Katsina

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari ƙauyen Barawa dake yankin karamar hukumar Ɓatagarawa ta jihar, inda suka yi mummunan ta’adi.

Rahotanni sun bayyana cewa yayin harin na ranar Lahadi, maharan sun kashe aƙalla mutun 4, tare da jikkata wasu da dama.

Wani mazaunin ƙauyen Barawa ya shaida wa manema labarai cewa yan bindigan sun farmaki kauyen ne a kan dandazon babura, kuma kowane ɗauke da makami.

Ya kuma kara da cewa yan bindigan sun kwashe fiye da mintuna 90 suka aikata ta’asar su ba tare da samun turjiya daga jami’an tsaro ba, wanda yasa suka samu damar cin karen su babu babbaka.

Har zuwa yanzun da muke kawo muku wannan rahoton, rundunar yan sanda reshen jihar Katsina ba tace uffan ba game da faruwar harin kauyen Barawa.

Sai dai wata majiya mai ƙarfi ta tabbatar da cewa bayan yan bindigan sun fice, an tabbatar da mutuwar akalla mutum 4 a harin, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kazalika har yanzun ba’a gano yawan adadin mutanen da yan bindigan suka ji wa raunuka kala daban-daban ba a yayin harin. Haka nan kuma babu wani cikakken bayani kan cewa ko yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutane ko sun saci kayayyakin amfani na yau da kullum.

Labarai Makamanta