‘Yan Bindiga Sun Sake Kaddamar Da Hari A Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar akalla mutum biyu sun rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da mutane 50 yayinda yan bindiga suka kai hari Unguwar Gimbiya dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Wani mai shaidan gani da ido wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa manema labarai cewa wannan hari ya auku ne da sanyin safiyar ranar Juma’a, a cewarsa yan bindigan sun kai hari gidaje akalla 13 kuma sai da suka kwashe sa’o’i biyu suna diban jama’a.

“Sun kai farmaki Ungwan Gimbiya dake Sabo, karamar hukumar Chikun dake Kaduna, sun kashe mutum 2, sun sace 50.”

Wani mazaunin daban, Gideon Jatau, ya bayyana cewar ba’a taba kai hari irin wannan ba a garin. Yace suna fuskantar lamarin sace-sacen mutane amma wannan ya yi munin gaske.

Yunkurin samun karin bayanai daga bakin Kakakin yan sandan Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya ci tura.

Labarai Makamanta