‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 100 A Cocin Kaduna


Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu gungun Ƴan bindiga sun sace sama da mutum 100 da hallaka mutum guda da kuma jikata wasu biyu a wani hari da suka kai wani coci a jihar a cewar shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar, Rabaran Joseph John Hayab.


Rabaran Hayab ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a Cocin Emanuel Baptist da ke ƙauyen Kakkaudaji a wajen garin Kaduna a ranar Lahadi, yayin da mutane ke tsaka da yin ibada.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa tana kan tattara wasu bayanai game da sabbin hare-haren da aka ƙara kai wa bayan na cocin kafin ta fitar da sanarwa gaba ɗaya.


Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da mabiyan ke tsakiyar ibada a cikin cocin nasu, inda suka suka abka musu ta harbe-harbe.

A baya ‘yan bindigar sun tarwasta tare da fattakar al’ummar yankin ƙauyen Kakkaudaji wanda ke kusa da Unguwan Ayaba, suka kuma mamaye shi bayan wani mummunan hari da suka kai.


Kungiyar Kiristoci ta Najeriya a jihar ta Kaduna ta nuna rashin jin dadinta game da yadda ake yawan kai hare-hare tare da sace-sacen jama’a don neman kudin fansa a jihar, duk kuwa da matakan da gwamnatin jihar ke cewa tana dauka.

Labarai Makamanta