‘Yan Bindiga Sun Sace Babban Limami A Abuja

Labarin dake shigo mana daga babban birnin Tarayya Abuja na bayyana cewar ‘yan Bindiga sun sace Babban limamin masallacin Yangoji da ke yankin Kwali a Abuja, Malam Abdullahi Abubakar Gbedako mai shekaru 59 tare da ‘ya’yansa biyu, Aliyu Usman Abubakar mai shekaru 22 da Ibrahim Abubakar mai shekaru 11.

An ruwaito, wani makwabcinsu mai suna Shuaibu, ya ce lamarin ya auku a daren Juma’a wurin karfe 11:47 na yamma yayin da aka sace shi. Sun bayyana da yawansu dauke da makamai sannan suka kutsa gidan babban limamin.

Ya ce wasu daga cikin ‘yan bindigan sun tsaya a wurare daban-daban inda suka dinga harbi a iska yayin da wasu uku suka tsallake katangar gidan limamin. “Sun dinga harbi tare da lalata kofofin gaban gidan kafin su shiga ciki inda dakin babban limamin ya ke tare da yin awon gaba da shi da ‘ya’yansa biyu,” .

Wani dan gidan babban limamin wanda ya bukaci a boye sunansa, ya bayyana cewa an kira su kuma masu garkuwa da mutanen sun bukaci kudin fansa har naira miliyan goma.

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan tarayya, DSP Adeh Josephine, ta tabbatar da satar limamin da ‘ya’yansa.

“Kwamishinan ‘yan sandan FCT, CP Sunday Babaji, ya yi kira ga jama’ar Yangoji da su kwantar da hankalinsu tare da samar da bayanan da za su taimaka wa ‘yan sanda wurin cafke wadanda ake zargi,” tace.

Labarai Makamanta