Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da dimbin matafiya daga cikin motocinsu a babbar hanyar Kaduna zzuwa Abuja da yammaci Lahadi, 21 ga Nuwamba, 2021.
Har yanzu ba’a san adadin wadanda aka sace ba. Wani faifan bidiyo da aka saki a kafafen ra’ayi da sada zumunta ya nuna motoci akalla biyu da aka kwashe wadanda ke ciki a tsakiyar titi.
A bidiyon mai daƙiƙa 31, an ji mai daukan bidiyon yana cewa: “Wayyo Allah, sun kwashe abokanmu, yanzu muke zuwa daga Kaduna. Yau 21 ga Nuwamba 2021.”
A riwayar da muka samu an bayyana ‘yan bindigan sun budewa matafiyan wuta ne misalin karfe 4 na yamma. Majiyar ta ce wanda suka yi kokarin guduwa an harbesu yayinda wadanda suka tsaya aka shiga da su cikin daji.
You must log in to post a comment.