‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Mahaifar Atiku Abubakar

Rahotanni daga garin Jada ta Jihar Adamawa Mahaifar tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma ɗan takarar Shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar na bayyana cewar wasu mahara dauke da bindiga sun kaddamar da wani hari a tsakar dare a garin Kojoli da ke karamar hukumar ta Jada inda suka yi awon gaba da wasu mazauna garin biyu.

Wani dan asalin garin, Dokta Umar Ardo, ya ce ‘yan bindigan sun isa garin ne da misalin karfe 1 na safiyar Lahadi kuma suka yi awon gaba da wasu fitattun mutane biyu bayan sun fatattaki ‘yan banga da ke yankin.

“A mummunan harin da ‘yan bindigar suka kai a safiyar Talata inda suka mamaye garin na Kojoli. Sannan suka afkawa Banja, wani yankin da galibi fulani suke zaune, cikin adadi mai yawa dauke da manyan bindigogi, cikin sauki suka fi karfin ‘yan banga na yankin.

“An ruwaito cewa sun tafi kai tsaye zuwa gidan Alhaji Bajika, Sarki Shanu na Kojoli, kuma suka yi awon gaba dashi. “Hakazalika, Dr Denis Malum, likitanmu na dabbobi, an sace shi a cikin gidan kiwonsa da ke kusa da garin Nyagang.

Don kiyaye bayanai, an sanar da ‘yan sanda abubuwan da suka faru kuma sun ce sun fara bincike,” in ji Ardo. Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar ya ci tura, saboda layin wayarsa ba ya shiga.

Labarai Makamanta