‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kwalejin Soji Dake Jaji

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki kwalejin Sojoji dake garin Jaji, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Wasu mazauna garin da aka zanta dasu sun bayyana cewa yan bindigan sun je garkuwa da wasu ma’aikatan kwalejin ne da kuma mazauna garin na Jaji dake hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Kwalejin Sojin dake Jaji shahararriyar makaranta ce da ake horas ds Sojojin kasa, na sama da kuma na ruwa a tsawon lokaci.

Wani mazauni Garin mai suna Malam Adamu, ya bayyanawa ‘yan Jarida cewa ‘yan bindigan sun dade suna addaban mazauna kwalejn da kauyukan dake makwabtaka da kwalejin. “Allah kadai ke karemu. Sun dade suna kwace mana shanu da yin garkuwa da jamaarmu.

Amma a magana ta gaskiya suna fuskantar Mummunan kalubale daga rundunar Sojoji wanda hakan ke haifar musu da koma baya inji shi.

Adamu yace.

Kwamandan kwalejin, Air Marshal Olayinka Alade, ya tabbatar da hakan ranar Laraba a Abuja yayinda ya kai ziyara hedkwatar Soji domin ganawa da shugaban hafsan Soji, Laftanan Janar Attahiru Ibrahim.

Kwamandan ya ce a ranar Talata, 13 ga watan Afrilu, ‘yan bindiga sun kora wasu shanu a bayan kwalejin bayan musayar wuta da Sojoji. Yace: “Ko jiya (Talata), na samu labarin wasu ‘yan bindiga sun kora shanu a bayanmu.

Wasu hafsoshinmu na atisaye a wajen. Sun yi arangama da yan bindigan kuma sai da sukayi musayar wuta a lokacin.”

Labarai Makamanta