‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Jarumin Fina-Finan Hausa

Wasu ‘yan Bindiga dauke da muggan makamai sun shiga gidan wani fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Nasiru Bello Sani, wanda aka fi sani da Nasiru Naba da misalin karfe 1:00 zuwa 2:00 na safiyar Laraba. Sun kuma yi awon gaba da sabuwar motar da ya saya kirar SUV da sauran kayayyaki masu daraja.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Naba ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan Bindigar wadanda ke dauke da bindigogi, sun shiga gidansa da ke Maidile a cikin garin Kano da karfin tuwo. Sannan suka tafi da sabuwar motarsa kwana daya da saya da kayayyakinsa masu muhimmanci, da dai sauransu.

“Na karbi motar ne a ranar da ta gabata. “Lambarta ma ba ta iso ba. “Godiya ta tabbata ga Allah, ba su cutar da kowa ba. Kawai dai sun dauke motar da muhimman kayayyaki,” in ji shi.

Jarumin ya ci gaba da bayanin cewa tuni ya kai rahoton lamarin ga hukumomin da ya kamata sannan kuma ya bukaci magoya bayansa da su saka shi a cikin addu’o’insu.

Labarai Makamanta