‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Mummunan Hari A Katsina

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewa akalla mutum 13 sun rigamu gidan gaskiya yayinda akayi awon gaba da dimbin wasu a mumunan harin da yan ta’adda suka kai jihar Katsina a daren Litinin da safiyar Talata.

An ruwaito cewa yan bindiga sun yi dirar mikiya ne a karamar hukumar Bakori da Funtua dake kudancin jihar Katsina. Garuruwan da aka kaiwa hari sun hada da Guga, Gidan Kanawa da Dukawa.

A hira da manema labarai wani shaidar gani da ido Nafiu Muhammadu ya bayyana cewa yan bindiga sun yi awon gaba da Hakimin Guga, Alhaji Umar, yayinda suka hallaka mutum 10.

“Suna zuwa suka fara harbi suna kona shagunan mutanen garin. Yayinda mutan suka fara gudu, yan bindigan suka fara harbi, hakan yayi sanadiyar mutuwar mutum 10 nan take.”

“Hakimin garin ya ki guduwa duk da cewa gidansa na nesa lokacin da aka kai harin, fuskantar yan bindigan yayi yana cewa mutanen su gudu. Lokacin suka kamashi.” “Sun kai shi gidansa inda suka kwashe kudi da kayan hatsi.” Hakimin kadai aka sace kuma har yanzu ba’a birne wadanda suka mutu ba.

Labarai Makamanta