‘Yan Bindiga Sun Hana Gudanar Da Jana’iza A Zamfara

Labarin dake shigo mana yanzu haka daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa kwanaki huɗu bayan kai wani hari da ya yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 12 a ƙaramar hukumar Maru cikin jihar har yanzu ‘yan bindiga sun hana a je a ɗauko gawarwakin don yi musu jana’iza.

Mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai ranar Juma’a a Daraga, ya yi sanadin tarwatsewar mazauna garin zuwa gudun hijira.

Rahotanni sun bayyana halin dar-dar da tashin hankali da jama’ar yankin ke ci-gaba da fuskanta tun bayan harin.

‘Yan sanda a Zamfara sun ce suna ƙoƙarin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi yankin da jihar gaba ɗaya.

Labarai Makamanta