‘Yan Bindiga Sun Hallaka ‘Yan Sanda Da Yin Awon Da Motar Kudi

Labarin dake shigo mana daga Ibadan babban birnin Jihar Oyo na bayyana cewa ‘Yan sandan jihar Oyo sun tabbatar cewa akalla mutum uku ciki har da ‘yan sanda biyu sun rasa rayukansu bayan da wasu ‘yan fashin da aka ce sun kai su goma suka sace wata motar ɗaukar kudi a yankin Idi-Ape na birnin Ibadan.

Rundunar ‘yan sandan ta ce motar ta dauko kudi ne yayin da ‘yan fashin suka kai mata hari da muggan makamai.

Daga nan ne ‘yan fashin suka buɗe wa jami’an ‘yan sandan da ke raka motar wuta, inda bayan haka suka tafi da kudaden da kawo yanzu ba a san yawansu ba.

Kwamishinar ‘yan sanda a jihar Oyo Ngozi Onadeko ta tabbatar da aukuwar fashin ta kuma ce daya daga cikin ‘yan sandan ya sami raunuka daga harbin da aka yi masa kuma ya cika daga baya a asibiti.

Kwamishinar wadda ta gana da manema labarai yayin da ta ziyarci wurin da fashin ya auku, ta kuma tabbatar da cewa wani dan sanda ya harbe daya daga cikin ‘yan fashin har lahira yayin da suke musayar wuta.

Yayin da ake musayar wuta wani harsashi ya kashe wani mutumin da ke wucewa a wurin. Wasu mutum hudu ciki har da ‘yan sanda biyu na asibiti, kamar yadda ‘yan sansa suka ce.

Sai dai gwamnan jihar ta Oyo Seyi Makinde ya mayar da martani kan fashin da ya auku a unguwar Idi-Ape ta birnin Ibadan.

Ga abin da ya ce a wani sakon Twitter, inda ya mika gofiyarsa ga wadanda suka kira lambar neman taimako ta 615 a jihar domin sanar da jami’an tsaro hali da ake ciki:

“Za mu ci gaba da inganta tsarin samar da tsaro da saurin kai dauki ta hanyar amfani da kayan aikin da muke da su a matakin gwamnatin jiha.”

Ya kuma ce, “muna mika godiyarmu ga dukkan jami’an tsaron da ke ci gaba da sadaukar da kansu domin kare mu.”

Labarai Makamanta