‘Yan Bindiga Sun Hallaka Wasu Daga Cikin Wadanda Suka Sace A Cocin Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘yan Bindigar da suka sace mutane 60 a cocin Emmanuel Baptist dake Kakau Daji, karamar hukumar Chikun, sun harbe mutum 2 har lahira.

A kwanakin baya ne ‘yan bindigan suka kai farmaki babban cocin suka kashe mutum ɗaya, kuma suka sace wasu.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Jumu’a, ɓarayin suka bukaci a kai musu buhunan shinkafa, jarkokin man gyaɗa, wanda a cewarsu zasu yi amfani da su wajen ciyar da mutanen.

Sha’anin tsaro dai na cigaba da samun matsala a jihar Kaduna, tun bayan matakin da Gwamnan jihar Nasiru El Rufa’i ya dauka na kin yadda da sulhu da ‘yan Bindiga, matakin dake shan yabo da suka daga jama’a.

Labarai Makamanta