‘Yan Bindiga Sun Gayyaci Buhari Zaman Sulhu

A cikin ‘yan watannin nan, ‘yan bindiga suna cigaba da cin karensu babu babbaka a yankin arewacin kasar nan inda suke kai hari tare da yin garkuwa da mutane, da aikata fyade ga Mata da kisa babu gaira babu dalili.

Sheikh Dr. Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama ya samu ganawa da wasu ‘yan bindigan a dajikan Zamfara da Kebby inda ya bukaci su ajiye makamansu, su rungumi zaman lafiya da sauran al’ummar ƙasa.

Sai dai a wata tattaunawa da ya yi da Jaridar Daily Trust, wani dan bindiga da ya rufe fuskarsa ya ce idan Buhari zai iya zagaya kasar nan dan yakin neman zabe, babu abinda zai hana shi zuwa su tattauna a kan zaman lafiya.

Ya ce tun farko an sasanta da kungiyarsa amma babu dadewa aka bar su a daji ba tare da jin wani labari ba, “Mun sasanta amma kuka bar mu a daji da bindigogi kuma babu sako ko dan aike. Me kuke tsammani? Ya kuke son mutum ya rayu? Duk alkawarurrukan da kuka yi mana baku cika ko daya ba,” yace. “Shugaban kasan da kan shi ya zo muka tattauna.

Lokacin da yake kamfen ai ya iya zuwa ko ina, me yasa ba zai iya zuwa yanzu ba? Kullum kashe mutane ake yi saboda bai dauka sasancin da muhimmanci ba.

“Babu ranar da ke fitowa ta fadi ba a kashe mutum a Zamfara, Neja, Kaduna ko Katsina ba.

Muna yabon Jonathan da ‘Yar’adua saboda Buhari ya kasa yin komai. Mun zabe shi ne saboda ya kawo gyara amma ya kasa.”

Labarai Makamanta