‘Yan Bindiga Na Tsaurara Kai Hare-Hare A Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun hallaka mutum 8 a wani sabon hari da suka kai kauyukan karamar hukumar Zangon Kataf, dake sashin kudancin jihar.

An ruwaito cewa kauyukan da harin ya shafa sun haɗa da Kibori da kuma Atagjah, a karkashin yankin Aytap. Wani shugaban yanki ya bayyana cewa wasu da ake zargin yan ta’addan Fulani ne sun farmaki Kibori da yammacin ranar Litinin.

“Daga zuwansu suka bude wuta kan mai uwa da wabi, inda suka kashe aƙalla mutum 5, sannan wasu da dama suka jikkata.” “Maharan sun kone gidajen mutane, kuma sun lalata kayayyakin abinci yayin harin.”

Yadda suka kai hari na biyu A cewar mutumin, ranar Talata da daddare, wasu da ake zargin makiyayan ne sun sake kai hari kauyen Atagjeh. Ya tabbatar da cewa harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku, yayin da wasu da dama suka ji munanan raunuka.

“Hari a yankin Aytap ya zama ruwan dare, kusan kowane kauye dake wannan yanki an taba kai hari, yayin da rayuwa da dukiyoyin mutane suka zama ba a bakin komai ba.” “Babban abin takaicin shine masu kai waɗan nan hare-haren fulani ne muke zargi, bata garin cikin su, kuma babu wasu jami’an tsaro da zasu kare mutane daga sharrin su.”

Har yanzun kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai ɗaga kiran wayan da ake masa ba, domin jin ta bakin hukumarsu.

Labarai Makamanta