‘Yan Bindiga Na Neman Mamaye Kaduna – Shehu Sani

Tsohon Sanata mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa Kwamared Shehu Sani a ranar Lahadi ya koka kan yadda ‘yan bindiga suka zama abin ban tsoro a wajen garin Kaduna.

Tsohon Sanatan ya yi magana ne dangane da yunkurin satar mutane da aka yi kokarin dakilewa a rukunin gidajen ma’aikatan tashar jirgin saman Kaduna da safiyar ranar Lahadi.

Wasu ‘yan bindiga ɗauke da manyan makamai da safiyar ranar Lahadi sun sake yin wani yunkuri na garkuwa da wasu ma’aikatan jirgin sama da ke zaune a rukunin ma’aikata na Hukumar Kula da Jiragen Sama na Tarayyar Najeriya (FAAN) a filin jirgin sama na Kaduna.

Wannan na zuwa ne kimanin makwanni biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka sami nasarar shiga filin jirgin saman kuma suka yi awon gaba da ma’aikata 11.

Sun yi awon gaba da mutanen da suka kunshi ma’aikatan hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya (NAMA) da iyalansu da kuma na Hukumar Kula da Yanayin Sama ta NiMET da kuma iyalansu su ma.

ShehuSani, a shafinsa na Twitter, ya bukaci hukumomi da su tsaurara matakan tsaro a filin jirgin saman domin kariya ga ma’aikatar, da ma’aikatanta da danginsu baki ɗaya.

Ya ce: “Ana bukatar taka tsantsan don kare Filin Jirgin Saman, da ma’aikatan sa da iyalan su. ‘Yan fashin sun kara nuna abin tsoro da karfin gwiwa a wajen garin Kaduna.”

Labarai Makamanta