‘Yan Bindiga: Gumi Ya Bar Jaki Ya Koma Dukan Taiki – Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya nuna damuwarsa kan ayyukan ‘yan fashi da ke addabar al’umman yankin arewa maso yamma.

Ya soki fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Abubakar Ahmad Gumi da ya nemi gwamnatin tarayya da ta yi wa ‘yan ta’addan, wadanda ke da alhakin mutuwar’ yan Najeriya da dama da lalata dukiyoyi a fadin kasar afuwa.

Gwamnan ya ce ya kamata Gumi ya yi wa masu laifin wa’azi kan illar kisan mutane ba nema masu afuwa ba, jaridar This Day ta ruwaito.

Masari ya sha alwashin cewa ba zai sake yin afuwa ga ‘yan fashi ba, yana mai cewa an ci amanar gwamnatinsa a shekarar 2016 da 2019 bayan sun bi ta wannan hanyar.

Ya ce mai laifi, mai laifi ne kuma babu abin da zai iya tabbatar da kisan ‘yan kasa da ba su ji ba basu gani ba.

Ya kara da cewa:

“Duba abokina, ɓarawo, ɓarawo ne kuma mai aikata laifi, mai laifi ne. Suna da laifi kuma ba za su iya ba da hujjar kashe rayukan bayin Allah ba.”

A wani labarin, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya caccaki fitaccen malamin addini, Sheikh Ahamd Gumi a kan tsokacinsa, inda yace a ninke yake a cikin duhu.

Fani-Kayode yayi martani ne a kan tsokacin Gumi inda yace in har za a iya yafewa masu shirya juyin mulki, me zai sa ba za a iya yafewa ‘yan binidga ba?

Fani-Kayode yace “Ta yuwu mu yiwa Hitler, Pol Pot, Stalin, King Leopard 11 na Belgium, Osama Bin Ladin, Al Bagdadi, Abubakar Shekau da duk wani wanda ya kashe mutane da yawa afuwa bayan mutuwarsu saboda tarihin da suka kafa a duniya.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply