‘Yan Bindiga Ba Su Da Manufa Kamar Boko Haram Da IPOB – Mohammed

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Sadarwa da Al’adu, Lai Mohammed ya ce yan bindiga da ke adabar yankin arewa maso yamma da wasu sassan arewa bata gari ne kawai, waɗanda ba su da wata manufa akan ta’addancin da suke yi.

Lai Mohammed ya ce suna da banbanci da yan Boko Haram da yan kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biafra wato IPOB, domin suna da manufofi da tuta akan ta’addancin su.

A cewarsa, ‘yan bindigan bata gari ne kawai amma ba su jayayya da ikon Nigeria a matsayinta na kasa mai yanci ko hadin kanta kamar IPOB da Boko Haram.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin hira da aka yi da shi a shirin ‘This Morning’ a gidan talabijin na TVC a ranar Litinin. Ya ce ba dai-dai bane a rika kwatanta ‘yan bindigan da IPOB da Boko Haram da ke da manufofi ko alaka da addini.

“Banbancin IPOB, Boko Haram shine a bangare guda, IPOB da Boko Haram suna da manufofi da suke son cimma, manufar cewa ba su son cigaba da zama ‘yan Nigeria, amma su ‘yan bindiga ba su da wannan manufar gaba daya.

“Babu wani banbanci tsakanin yan bindiga da sauran bata gari sai dai sun fi su tsananta barna. “Yan bindiga ba su taba cewa ba su yarda da kasancewar Nigeria a matsayin kasa ba, kawai bata gari ne masu laifi.”

Labarai Makamanta