‘Yan Adawa Ne Ke Jifa Na Da Ta’addanci – Pantami

Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Pantami, ya ce zarge-zargen cewa yana da alaka da masu tsattsauran ra’ayi karya ce kawai da wasu ‘yan adawa suka kirkira domin su ɓata mishi suna.

Pantami ya fadawa jaridar Premium Times a wata hira ta musamman a ranar Juma’a,  cewa mutanen da ke adawa da yadda gwamnati ke hada lambar NIN da lambobin wayoyi sune ke yada zargin domin wata manufa ta son zuciya.

“Ba na shakka game da wannan. Yana da alaƙa da Lambar Shaida ta ‘yan ƙasa. Kun san abu daya? An fara wannan tsarin a shekarar 2011, ba ta ci nasara ba. Me ya sa? An yake ta.”

Ya yi ikirarin cewa wasu tawaga sun dauki aniyar dakatar da manufar yin rajistar shaidar zama dan kasa ga dukkan ‘yan Najeriya da kuma wadanda ke zaune a kasar.

Ministan ya ce: “A 2015, ya fito, bai yi nasara ba. A cikin 2018 akwai lokacin da aka yi ganawa tsakanin gwamnati da kamfanonin sadarwar wayoyin hannu. Kuma a zahiri an sanar da cewa ta hanyar yarjejeniya da gwamnati, wa’adin ya kasance watan Janairun 2018.

Yana nan kan yanar gizo, zan nuna maku idan kuna so. Zuwa Janairu 2018, ba a aiwatar da shi ba, saboda akwai masu adawa da shi. Akwai tawaga masu adawa da shirin.

“Yanzu sun fara zuwa da labarin cewa mutane na zuwa daga kasashe makwabta don yin rijista. “Abin da suka kasa fahimta shi ne cewa Lambar NIN ta kasa ba ta yan Najeriya kadai ba ce; kowa a Najeriya zai iya samunta.” Ministan ya bayyana cewa ba zai bar hare-haren da aka kai masa su dauke hankalinsa daga aikinsa ba.

Labarai Makamanta