Yaki Da Rashawa: Gwamnatin Buhari Ta Saki Manyan Barayin Gwamnati Biyu

Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sako wasu tsoffin gwamnoni da aka samu dumu-dumu da laifin rashawa.

An sako tsoffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba, wato Sanata Joshua Dariye, da Jolly Nyame daga babban gidan Kurkukun Kuje da ke birnin tarayya Abuja.

Wannan na zuwa ne watanni uku bayan afuwar da majalisar kasa karkashin jagorancin shugaban kasar Muhammadu Buhari ta yi a ranar 14 ga Afrilu, 2022.

Wata majiya daga gidan Kurkukun ta shaida wa jaridar Dailytrust cewa an saki tsoffin gwamnonin ne da misalin karfe 2:15 na ranar Litinin.

Haka kuma an sake wasu fursunoni uku daga gidan Kurkuku da ke Suleja dake jihar Neja.

Nyame dai zai yi zaman gidan yari na shekaru 12 ne bisa samunsa da laifin karkatar da Naira biliyan 1 da miliyan 64 a lokacin da yake gwamnan Taraba, yayin da Dariye ke zaman gidan yari na matsayin shekaru 10 a kan zambar Naira biliyan daya da miliyan 126.

Matakin da majalisar ta dauka na sakin ‘yan siyasar biyu ya haifar da cece-kuce daga ‘yan Najeriya da kungiyoyin rajin kawo karshen rashawa.

Akasarin jama’ar da aka zanta dasu sun soki matakin da gwamnatin Buhari ta ɗauka na sakin su, inda suka bayyana sakin nasu a matsayin wata alama dake nuna babu gaskiya a ikirarin gwamnatin tarayya na yaki da rashawa.

Labarai Makamanta