Yaki Da Rashawa: Annobar Korona Ta Mayar Mini Da Hannun Agogo Baya – Buhari

Labarin dake shigo mana daga Birnin Dubai na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga Shugabannin Duniya su hada karfi da karfe wajen fuskantar kalubalen da al’ummar duniya ke fuskanta.

A jawabin da ya gabatar ranar Juma’a, 3 ga Disamba, yayin taro EXPO 2020 dake gudana a Dubai, Shugaban Buhari ya bayyana cewa hada kai zai taimaka wajen kawar da annobar Korona a fadin duniya.

A jawabin da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar a shafinsa na Facebook, Shugaba Buhari ya bayyana yadda Annobar Korona ta janyowa tattalin arzikin Najeriya koma baya da kuma yaki da rashawa.

“Shugaba Buhari ya bayyana wa EXPO cewa Najeriya, kamar sauran kasashen duniya sun illaltu da annobar COVID-19, wanda ya tsananta lamarin tsaro, yaki da rashawa da kuma fadada tattalin arzikin kasar.” “Amma duk da haka, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarori cikin kankanin lokaci.”

Annobar Korona ta kawo min cikas wajen yaki da rashawa, Buhari ga Shugabannin duniya a Dubai Hoto: Femi Adesina Source: Facebook Buhari ya godewa Shugaban kasar UAE

Buhari ya mika godiyarsa ga Shugaban kasar ta UAE, Sheikh Khalifa Bin Zayed Al Nahyan, bisa gayyatarsa wannan taro kuma da ya samu halartan ‘ranar baja kolin Najeriya.’ Buhari yace wannan dama ta baiwa Najeriya daman nunawa duniya itace kasa a nahiyar Afrika mafi girman tattalin arziki.

Labarai Makamanta