Yakar Yunwa: Bankin Duniya Zai Ba Afirka Tallafin Dala Biliyan Biyu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Washington DC na ƙasar Amurka na bayyana cewar Bankin Duniya ya amince da tallafin kuɗi na sama da dala biliyan biyu ga ƙasashen Gabashi da Kudancin Afirka, don taimaka musu wajen bunƙasa wadatar abinci.

A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce kimanin mutum miliyan 68 a yankin ke fuskantar matsalar ƙarancin abinci da barazanar yunwa.

Ya ƙara da cewa matsalolin sauyin yanayi da tabarbarewar tattalin arziki da siyasa da rikice-rikice na kara ƙamari.

Yaƙin Ukraine ya ƙara haifar da matsalar ƙarancin abinci a fadin duniya.

Bankin Duniya ya bayyana Habasha da Madagascar da suka daɗe suna fama da fari, a matsayin kasashen da za su karbi kason farko na tallafin.

Labarai Makamanta