Yajin Aikin Likitoci: Ministar Kudi Za Ta Bayyana Gaban Majalisa

Rahotonni da muke samu daga majalisar dokokin tarayya na bayanin cewar Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana aniyar majalisar na gayyatar ministar kuɗi, Zainab Ahmed, domin tazo ta musu bayani akan wasu buƙatun da ƙungiyar Likitoci ta ƙasa NARD ta shigar na dalilin tsunduma yajin aiki a kwanakin baya.

A ranar Asabar ɗin data gabata ƙungiyar likitoci NARD ta janye yajin aiki da ta fara tun 1 ga watan Afrilu bayan ƙulla yarjejeniya da gwamnatin tarayya.

Likitocin dai sun shiga yajin aiki ne saboda rashin cika musu alƙawurra da gwamnatin tarayya tayi na kuɗaɗen da suke binta, da sauran wasu bukatu da suka bayyana.

A jawabin da yayi lokacin da suka yi taro da Ƙungiyar ta NARD ranar Talata, Shugaban Majalisar wakilai Gbajabiamila, ya ce majalisarsu zata gayyaci ministar kuɗi don su tattauna da ita kan yadda za’a kutsa buƙatun NARD a ƙarin kasafin kuɗi da ake yi.

Kakakin majalisar ya ƙara da cewa: “Ko kundin tsarin mulki ya yi magana a kan ayyuka masu muhimmanci, amma babu wani aiki da yafi kare lafiya muhimmanci.” “Za mu saka ido don ganin an yi abinda ya dace kan dukkan buƙatun ƙungiyar  NARD.”

“Za mu yi duk abinda zamu iya kuma muke da damar yi, zamu gayyaci ministar kuɗi a mako mai zuwa saboda mu tattauna yaza’a yi mu saka waɗannan buƙatun naku a ƙarin kasafin kuɗi.”

Kakakin majalisar ya ƙara cewa sun zaɓi su zo su gana da shugabannin Likitocin ne a hedkwatar su don su nuna jin daɗin su kan janye yajin aikin da suka yi.

“Ziyarar da muka kawo muku na nuni da cewa muna tare da ku saboda muhimmancin likitoci bazai misaltu ba, kuma muna godiya a gareku da kuka janye yajin aiki.” “Mun zo nan ne mu gode muku bisa janye yajin aiki kuma mu ƙara baku tabbacin majalisar mu tare da majalisar zartarwa, zasu yi duk abinda ya kamata ayi.”

A jawabinsa, shugaban ƙungiyar likitocin ya nuna jin daɗinsa da ‘yan majalisar wakilan suka kai musu ziyara, Ya kuma gode ma majalisar kan saurin shiga maganar da ta yi wanda hakan yasa ƙungiyar ta janye yajin aikin.

Labarai Makamanta