Yajin Aikin ASUU: Zan Kori Dukkanin Malaman KASU – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai yayi barazanar sai ya kori duka malaman jami’ar jihar Kaduna KASU, muddin ya bincika ya gano sun shiga yajin aikin da ASUU ke yi.

Muryoyi ta ruwaito Gwamnan wanda ke hirar kai tsaye da yan jarida a daren ranar Laraba a Kaduna ya ce a baya ya tsaida albashin ma’aikatan jami’ar amma sai aka shaida masa cewa basu shiga yajin aiki ba

“Ma’aikatan jami’ar jihar Kaduna, KASU basu da matsala da Gwamnatin jihar Kaduna domin komi suka nema munyi masu, hakanan duk bukatun ASUU jihar Kaduna mun biya masu, don haka bamu ga dalilin da zai sa su kulle makaranta su shiga yajin aikin ASUU wacce ke fada da Gwamnatin tarayya ba”

“Don haka wallahi, wallahi nasa a bincika mini kuma muddin aka bani rahoton cewa KASU na yajin aiki to sai na kori duka ma’aikatan jami’ar na dauki wasu”

El-Rufai ya ce a baya sun taba shiga yajin aiki ya sa aka tsaida albashinsu daga bisani suka ce basa yajin aiki yasa aka biyasu ya gargadesu kusan sau Biyu don haka wannan karon korace, zai kore su gaba daya tunda dama dokar kasa cewa tayi duk wanda ya shiga yajin aiki a hanashi albashi.

Labarai Makamanta