Yajin Aikin ASUU: Dalibai Sun Gudanar Da Zanga-Zanga

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ɗaliban jami’o’in Najeriya na ci gaba da zanga-zangar lumana a sassan ƙasar daban-daban biyo bayan yadda yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsawon lokaci.

Ko a ranar Litinin 20 ga watan Satumba ɗaliban sun toshe hanyar shiga filin jirgin sama na Murtala Muhammad tare da wasu manyan hanyoyi, wani lamari da ya haifar da cikas ga sufurin jiragen.

Hakan dai wani ƙoƙari ne da suke yi domin matsawa gwamnatin ƙasar lamba don ta magance yajin aikin da malaman jami’o’in Najeriya ke ci gaba da yi, sama da wata shida.

Daliban sun ce za su toshe hanyoyin da za su kai ga babbar tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas, da kuma babban kamfanin man fetur na NNPC da ke babban birnin ƙasar, Abuja.

Shugaban ƙungiyar ɗaliban jamio’i na ƙasar Comrade Umar Faruk Lawan, ya shaida wa BBC cewa daga cikin dalilinsu na yin zanga-zangar shi ne don jawo hankalin gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace a kan yajin aikin da aka shafe watanni ana yi.

“Idan aka duba kalanda yau wajen wata takwas kenan ana yajin aiki a jami’o’in Najeriya gaba ɗaya. Idan ba mu yi zanga-zangar ba har aka fara tafiyar siyasa a ranar 28 ga watan Satumban nan, to gaskiya babu wanda zai saurari ɗalibai.

“Za su ci gaba da harkar siyasarsu ne, sai an gama siyasa sannan za su waiwayi ɗalibai,” in ji shi.

Ya jaddada cewa shi ya sa suke wannan tattaki don jawo hankalin gwamnati ta saurari batun ɗalibai.

“Mun so mu yi a Abuja ma amma ana ta ba mu haƙuri da la’akari da matsalar tsaro da ake fama da ita a ƙasar. Shi ya sa muka haƙura da yi a can. Amma muna nan muna shiri, za mu iya yi da kowane lokaci.”

Ya ce suna toshe hanyoyin manyan wurare na ƙasar ne saboda hakan ne kawai zai jawo hankalin hukumomi kan abin da suke yi har a saurare su .

“Idan ba mu yi haka ba babu mai sauraronmu,” ya ce.

Sai dai mutane da dama masu fafurukar neman abin rufin asiri sun koka cewa wannan toshe hanyoyi na yin mummunan tasiri kan harkokinsu na yau da kullum.

Amma Kwamared Umar Faruk ya ce masu kuɗi da masu mulki lamarin ya fi shafa, kuma dama su ne ake son jawo hankalinsu kan batun.

“Muma abin ya fi shafa ai, wata bakwai zuwa takwas babu karatu,” ya ce.

Shugaban daliban ya ƙara da cewa ya yi amanna ba gwamnati ce kadai mai laifi a batun yajin aikin ba, ita ma ƙungiyar malamai ta ASUU da nata laifin.

“Shi ya sa ma mako biyu da suka wuce na kai gwamnati da ita ASUU ƙara kotu, saboda hakan zai sa dole su zo a zauna a cimma matsaya,” a cewar Kwamared.

Ya ƙara da cewa a yanzun ma ba su fitar da tsammanin cewa kafin makon nan ya ƙare za a cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu ba.

Labarai Makamanta