Yajin Aikin ASUU: Ba Za Mu Biya Albashin Watanni Shidda Ba – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ministan ilimi Adamu Adamu ya ce batun biyan malaman jami’o’i albashinsu na tsawon watannin da ba su yi aiki ba shi ne kaɗai abin da ya rage ba a cimma ba a yarjejeniyar ASUU da gwamnati.

Minsitan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Sannan Malam Adamu Adamu, ya ce hakkin malaman jami’o’i ne su biya ɗalibai diyya saboda ɓata musu lokacin da suka yi tsawon wata shida a yayin da suke yajin aikin da ba gwamnati ta sa a yi shi ba.

Adamu Adamu, ya ce ya kamata daliban da yajin aikin ya shafa su kai kungiyar kotu don neman fansa a kanzaman banzan da aka tilasta musu a gida.

Labarai Makamanta