Yajin Aiki: Gwamnati Ta Yi Barazanar Hana Likitoci Albashi

Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar tsaida albashin duk wani likitan da ya tsunduma yajin aiki tun a ranar Alhamis da ta gabata.

Ministan Kwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka, cikin wata tattaunawa da ake yi da shi a gidan talbijin.

“Zuwa ranar Talaba zan sake gayyatar su mu sake zaunawa. Amma idan su ka kekasa kasa su ka ki janyewa din, zan nuna masu ba su isa ba.” Inji Minista Ngigel.

“Ai akwai wani makami a dokar aiki, wanda zan rika zabga masu duka da shi. Wato ‘idan ba ka yi aiki ba, to babu biyan ku albashi.”

Dokar aiki dai ta ce ko ma’aikata sun tafi yajin aiki, to wajibi ne a rika biyan su alabashi, matsawar a kungiyance su ka tafi yajin aikin.

Sai dai kuma dokar ta yi karin hasken cewa gwamnatin tarayya za ta iya dakatar da albashin wadanda su ka tafi yajin aiki, idan ta yi amanna cewa masu yajin aikin ba su da wani kwakkwaran dalilin daina aiki, kuma idan gwamnatin ta gamsu cewa yajin aikin haramtacce ne, ba shi da dalili.

Su dai likitocin Najeriya sun tafi yajin aiki saboda neman biya masu bukatun da su ka ce wajibi ne a biya masu.

Sun yi korafin ana wasa da rayukan su, kuma likitocin kungiyar NARD 17 sun mutu a Babban Asibitin Ibadan, yayin da a cikin Yuli, 2020 aka sanar cewa likitoci 812 su ka kamu da cutar korona.

Ita ma kungiyar Manyan Likitoci ta Kasa ta bayyana cewa mambobin kungiyar 20 cutar korona ta kashe a wurin kokarin su na ceton rayukan masu fama da cutar korona.

Haka kuma an ruwaito cewa akalla aikin kula da masu cutar korona ya yi sanadiyyar kashe mana likitoci 17, shi ya sa muka shiga sahun yajin aiki –Shugaban Likitocin Badun

Shugaban Kungiyar Likitocin Babban Asibitin Jami’ar Ibadan (UCH), Temitope Husein, ya bayyana cewa sun shiga cikin sahun yajin aikin da uwar kungiyar su ta likitocin Najeriya NARD ta shirya, saboda likitoci abokan aikin su 17 ne su ka rasa rayuwar su sakamakon aikin kula da masu cutar korona.

Hussein a kokarin san a nuna wajibcin tafiyar da su ka yi yajin aiki a karkashin kuniyar likitoci ta kasa Nard, ya bayyana cewa tun bayan mutuwar likitocin 17, har yau iyalan su ba su samu kudaden inshora din da ake bai wa iyalan mamacin da ya mutu a wurin aiki ba.

Ya kara da cewa likitocin sun tafi yajin aiki ne domin neman a biya su hakkin su da aka danne wa wasu yan uwan su likitoci a kasar nan.

Hakkokin sun hada da albashin da wasu ke bi har yau ba a kai ga biyan su ba, sannan kuma akwai alawus-alawus da kuma bukatar da su ke da ita na kara masu alawus din saida rayukan su da su ke yi da sauran su.

Labarai Makamanta