Yadda Za A Farfaɗo Da Martabar Ilimi A Arewa – Bintaliya

Shahararriyar ‘yar kasuwa kuma shugaban rukunin bintaliya groups, Hajiya Binta Hamidu da aka fi sani da Bintaliya ta bayyana wasu hanyoyi da za a iya bi wurin ganin an shawo kan tabarbarewar Ilimi a arewaci dama kasar baki daya.

Hajiya Bintaliya ta bayyana hakan ne a cikin shirin kwabon ka jarinka da Aisha M Ahmad ke gabatarwa a gidan talbijin da radio na Liberty.

Hajiya Bintaliya ta bayyana ilimi a matsayin jigo na rayuwar ‘dan adam, kuma saida ilimi ne mutum zai iya anfanar kansa da duniya baki daya.
” Da take tsokaci akan muhimmancin koyawa yara ilimin na’ura mai kwakwalwa domin su anfani kansu da al’umma baki daya a nan gaba. Bintaliya ta bayyana cewa kusan kimanin shekaru 20 kenan tana koyawa yara ilimin kwamfuta a bangarori da dama, Wanda inda gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi zasu maida hankali wurin samarwa yaran mu dake makarantu kayayyakin koyan ilimi na zamani da an samu sauki sosai wurin fuskantar kalubalen da ilimi ke fuskanta musamman sakamakon bullar annobar covid 19.

”Domin ta hanyar na’urar kwamfuta dalibi yana gida zai iya samun ilimi a saukake ta manhajar da gwamnati ta samar Wanda hakan ba zai kawo tsaiko ga fannin ilimin ba kamar yadda muke gani a halin yanzu.

Saboda matsalolin da aka samu ne na bullar annobar covid 19 ne Bintaliya group ta kirkiro da shiri na musamman mai suna SAFE SCHOOL INITIATIVE. Shiri ne na musamman wanda bintaliya group foundation ke bin anguwanni da gidaje suna rabawa yara littattafan koyan karatu da rubutu domin zaman da sukeyi a gida sakamakon bullar cutar korona zaisa su manta da abubuwa da dama da ake koya masu a baya sakamakon zaman gida. Kuma iyaye da yawa ba kowa bane keda halin koyawa yaransa darasi na musamman a gida ko ya biya a koya masa yayin zaman gida sakamakon cutar covid 19, wannan dalili yasa gidauniyar mu ta fitar da makudan kudade wurin aiwatar da wannan shiri inda ko a makon da ya gabata an jiyo inda shugaban cibiyar kasuwanci ta duniya Dr Ngozi Okonjo Nwella ta jinjinawa shirin namu a ziyarar da ta kawo fadar shugaban kasa dake babban birnin taryayya Abuja.

Duk da taimakon da kungiyoyi irin namu keyi a kasar nan bazai iya kaiwa ga dukkan mabukata ba, Amman muddin gwamnonin yankin mu na arewa suka maida hankali wurin aiwatar da dokar ta baci kan harkar ilimi musamman wurun tilasta anfani da na’ura mai kwakwalwa da kuma Samar da ingantattun kayayakin aiki na zamani, insha Allahu za a samu cigaba kuma hakan zai kawo karshen koma bayan da yankin mu na arewa ya dade da samu musamman a yankin mu na arewa.

Labarai Makamanta