Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Yadda Jaruma Fadila Muhammad Ta Rasu – Mahaifinta

Rasuwa fitacciyar jaruma Fadila Muhammad a daren jiya ta girgiza masana’antar finafinai ta Kannywood matuƙar gaske.

Mujallar Fim ta gano cewar ta rasu ne a jiya Juma’a, 28 ga Agusta, 2020, da misalin ƙarfe 11:00 na dare a cikin motar mahaifin ta a lokacin da ya ɗauke ta zai kai ta asibiti.

Da ma ta na fama da ciwon zuciya. Tun a shekaranjiya Alhamis ciwon ya tashi, aka kai ta asibiti ta ɗan samu sauƙi aka dawo da ita gida a ranar. A daren jiya kuma ciwon ya yi dawowar ƙarshe.

Fadila ta rasu ta na da shekara 27 a duniya.

An yi mata sallah da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar yau a nan gidan iyayen ta da ke Fagge Close, Unguwar Dosa, Kaduna, daga nan aka kai ta makwancin ta.

Marigayiyar ta kai kimanin shekara takwas a Kannywood, inda ta yi finafinai da dama.

An fi sanin ta da fitaccen fim ɗin ‘Hubbi’ na kamfanin Adam A. Zango, kuma ta fito a fim ɗin sa na ‘Basaja’.

Wannan mutuwa ta girgiza ‘yan fim matuƙa, kowa na ta yi wa Ummi addu’a, musamman a soshiyal midiya inda da yawa su ka riƙa saka hotunan ta da kuma guntayen bidiyo daga waƙoƙin ta a finafinai.

Wakilin mujallar Fim, wanda ya halarci jana’izar Ummi, ya zanta da mahaifin marigayiyar bayan an dawo daga maƙabarta game da wannan babban rashi.

Malam Muhammad ya ce, “Wannan rashi da mu ka yi babu abin da zan ce sai Allah ya jiƙan ta da rahama, Allah ya sa Aljannar Firdausi ta zama makoma a gare ta” Ya na faɗin haka sai ya fara kuka.

Ya ci gaba da cewa: “Wannan yarinya babu abin da zan ce mata sai Allah ya saka mata da alheri, Allah ya yi mata sakayya da gidan Aljanna.

“Yadda wannan yarinya ke yi min biyayya, Allah na gode maka da ka amshi ran wannan yarinya a hannu na!”

Ya ci gaba da faɗa wa wakilin mu cewa: “Kai dai ganau ne, tun daga gida zuwa gidan ta na gaskiya ka ga irin ɗan’adam da su ka halarci jana’izar ta.

“Kuma rasuwar yarinyar nan, in da Allah ya ƙadarta sanadiyyar wani abu ne na ɓacin rai, ka ga mutum ba zai damu ba; za ka ga ka haifi yaro, in ya mutu ba ka damu ba ko kuma ka ce gara a kashe shi ma. Amma ka ga ‘yan’uwa da abokan arziki da iyaye kowa na zub da hawaye. Na san dai wannan yarinya Alhamdu lillahi!

“Kuma kullum addu’ar ta Allah ya karɓi rayuwar ta kafin nawa, don ba ta son ni in rasu in bar ta.

“Abin da zan rinƙa tunawa game da ita, a kullum burin ta me za ta yi min da zai sa na samu sauƙin rayuwa.”

A game da maganar su ta ƙarshe da Fadila, Malam Muhammad ya ce: “Jiya na ɗauke ta zan kai ta asibiti, ta ce min, ‘Baba ka yi haƙuri, na ga ka na ta wahala da ni.’ Sai na ce mata, ‘Ai ba siya ki ka yi a kasuwa ba, fata na dai Allah ya sa mu yi ƙarshe mai kyau daga ni har ke.’ Wannan abu ba zan taɓa mantawa da shi ba!”

A nan ma sai shauƙi ya fizge shi, ya shiga kuka.

Daga baya, sai dattijon ya iske wakilin mujallar Fim a inda ya ke tsaye, ya ba shi saƙo zuwa ga ‘yan fim duka, ya ce: “Ku ke hulɗa da ‘yan fim ɗin nan da sauran jama’a. Don Allah ku taimake ni ku faɗa wa mutane in da wanda ke da wani alƙawari na bashi tsakanin shi da Ummi, don Allah kada ya yi ƙasa a gwiwa, ya zo har gida na ya sanar da ni.”

Mujallar Fim ta tuntuɓi shugabar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta ƙasa (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Hajiya Fatima Ibrahim (Lamaj), wadda ita ce sanadiyyar shigar marigayiya Fadila harkar fim, don ‘yar kamfanin ta ce, bayan zuwan su Fati Washa kamfanin, ya tambaye ta game da wannan rashi.

Sai Lamaj ta ce, “Allahu Akbar! Babu abin da zan ce sai dai in yi wa Allah godiya domin shi ne ke raya mutum, kuma shi ke ɗaukar abin sa. Ina ganin bayan iyayen ta, sai ni aka yi wa wannan rashi, don babu wanda ya ji wannan mutuwar kamar ni.

“Kwana biyun nan ba na iya bacci, sai bayan asuba na ke samun bacci, shi ya sa ban samu zuwa jana’izar ba, don ban san da rasuwar ba, ina dai jin kai na wani iri, na rasa gane abin da ke damu na, ashe labarin rasuwar Ummi zan ji!

Exit mobile version