Ya Zama Wajibi A Yi Gaggawar Zaman Mukabala Da Abdul-Jabbar – Sheikh Yabo

Shahararren Malamin addinin Musulunci a Nigeria, Sheikh Bello Aliyu Yabo Sokoto, ya yi kira ga gwamnatin Kano, da ta gaggauta sanya zama tsakanin Malaman Kano da Zindiƙi Abduljabbar.

Shehin Malamin ya bayyana cewa: “Bai yiyuwa a taɓa mutuncin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallama), sannan a shashantar da maganar, domin mun ji wani ya zagi Buhari, Gwamna Ganduje ya ɗaukar masa mataki cikin gaugawa, shin kai Ganduje kana nufin mutuncin Buhari ya fi na Manzon Allah?”.

Shehin Malamin ya ci gaba da cewa: “Ba za mu daina wannan magana ba har sai an yi zaman nan”.

Shehin Malamin ya ƙara da cewa: “Duk wanda ya karɓi kuɗi don lalata wannan magana Allah Ya sa su zama bala’i a gare shi.

Labarai Makamanta